Ministan aikin gona da raya karkara na kasar Audu Ogbeh ne ya yi kiran yayin wani taron kungiyar daliban fannin nazarin ayyukan gona ta kasar, da ya gudana a Abuja babban birnin kasar.
Audu Ogbeh ya ce shigar da karin matasa cikin harkokin gona, zai bunkasa kokarin kasar, na kara yawan albarkatun gona da take fitar da su tare da samun wadatuwar abinci.
Ministan ya ce gwamnati na kokarin amfani da ayyukan cibiyoyin bincike da jami'o'in nazarin aikin gona a yunkurinta na samar da fasahohin zamani da za su taimakawa matasa manoma inganta ayyukansu. (Fa'iza Mustapha)