in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani sabon rikicin kabilanci ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 11 a Nijeriya
2017-05-17 10:29:45 cri
Akalla mutane 11 ne suka mutu sanadiyyar wani sabon rikicin kabilanci da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a jihar Taraba dake arewa maso gabashin Nijeriya.

Shugabn kungiyar manoma a yankin Zaki David –Gbaa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa mutane da dama sun jikkata sanadiyyar rikicin da ya barke tun ranar Lahadin da ta gabata .

Ya ce galibin wadanda da aka kashe a rikicin da ya bazu zuwa a akalla kauyuka biyar na yankin Bali manoma ne.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce zuwa yanzu gawarwaki uku aka gano saboda yadda yankin ke da nisa.

Kakakin rundunar David Misal ya shaidawa manema labarai cewa, tuni aka tura jami'an kwantar da tarzoma kauyukan da rikicin ya shafa domin dawo da zaman lafiya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China