in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yanke kudurin karfafa ayyukan tawagar kiyaye zaman lafiya dake Mali
2016-06-30 11:09:41 cri
Jiya Laraba 29 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya yanke kudurin tsawaita wa'adin aikin tawagar kiyaye zaman lafiya ta MDD dake kasar Mali har zuwa shekara daya, yayin da kuma za a kara karfafa kwarewarta wajen gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

A yayin cimma wannan kuduri, kwamitin ya nuna yabo ga tawagar kiyaye zaman lafiya ta MDD dake Mali kan babbar gudummawa da ta bayar, yayin da kuma ya nuna juyayi ga ma'aikatan da suka rasu sakamakon aiki mai hadari da suka gudanar, haka kuma, ya yi allah wadai da hare-haren da aka kai ga sojojin kiyaye zaman lafiya.

Cikin kudurin, kwamitin ya tsawaita wa'adin aikin tawagar har zuwa ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 2017, kuma ya kara adadin dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD daga 11240 zuwa 13289, yayin da kuma ya kara adadin 'yan sanda daga 1440 zuwa 1920.

Bugu da kari, an ce, aikin dake jiran wannan tawagar shi ne na nuna goyon baya ga bangarori daban daban na kasar Mali da su aiwatar da yarjejeniyar sulhu da zaman lafiya ta Mali, musamman ma taimaka wa gwamnatin kasar wajen farfado da mulkinta a dukkan fadin kasar

Bugu da kari, cikin kudurin, ana sa ran babban magatakardan MDD Ban Ki-moon zai dauki matakan karfafa yanayin tsaron tawagar, kamar kyautata kwarewarta wajen samun labaran da abin ya shafa, samar mata horaswa da kayayyakin aiki, karfafa ayyukan ba da jinya gare ta da sauransu, ta yadda za ta iya gudanar da ayyukanta yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China