Wata sanarwa da kwamitin na tsaro ya fitar, ta ce an kai harin wani sansanin MINUSMA dake birnin Timbuktu, abu ne mai matukar tada hankali. Tuni dai kungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin ta ce ita ce ta kaddamar da harin.
Mambobin kwamitin na tsaro dai sun ja hankalin gwamnatin Mali, da ta gaggauta gudanar da bincike game da aukuwar lamarin, tare da gurfanar da wadanda suka kitsa shi gaban kuliya, suna masu bayyana harin, a matsayin laifin da ka iya zama na yaki a karkashin dokokin kasa da kasa.