in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 19 sun mutu sanadiyyar fashewar wani abu a Manchester
2017-05-23 09:42:27 cri

Kawo yanzu, mutane 19 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da kusan 50 suka jikkata, sanadiyyar fashewar wani abu a Manchester na kasar Birtaniya jiya da daddare.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ofishin 'yan sandan yankin Greater Manchester ya fitar yau da safe, inda ta ce, a yanzu an dauki al'amarin a matsayin harin ta'addanci har zuwa lokacin da aka tabbatar da sabanin hakan.

Gab da karfe 10:35 na jiya da dare agogon Manchester, aka sanar da 'yan sanda fashewar wani abu a filin wasanni na Manchester, a lokacin da ake tsaka da gudanar wasan nishadi.

Filin wasan na Manchester na iya daukar mutane 21,000, kuma kafafen yada labarai sun ruwaito cewa, filin a cike yake a lokacin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China