Du Qinglin ya bayyana cewa, mu'amalar dake tsakanin majalisun tattalin arziki da zamantakewar al'umma na kasashen biyu wani muhimmin bangare ne na raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Majalisar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin za ta kiyaye yin mu'amala tare da bangaren Cote d'Ivoire bisa tunanin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka mai dacewa da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, a kokarin samar da gudummawa wajen aiwatar da sakamakon da aka samu a gun taron koli na Johannesburg na dandalin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka tare da raya dangantakar dake tsakanin Sin da Cote d'Ivoire.
A nasa bangare, Diby ya nuna yabo ga sakamako da aka samu a taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya hanya daya", kana yana fatan majalisun biyu za su kara taka muhimmiyar rawa wajen inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Zainab)