Wasu sojojin musamman dake sansanin sun yi harbi cikin iska, daga baya suka mamaye manyan titunan wurin, inda suka kori jama'a zuwa gida. Haka kuma an rufe hukumomin gwamnati da makarantu da kantuna dake wurin. Bayanai na nuna cewa, wadannan sojoji son yi hakan ne don nuna rashin jin dadinsa ga matakin da gwamnati ta dauka a baya na baiwa wasu sojoji da suka tayar da bore kudi.
A jiya da yamma ne, hafsan hafsoshin sojojin kasar Cote d'Ivoire da babban hafsan sojojin musamman na kasar suka tashi zuwa Adiaké don yin shawarwari da wakilan sojojin da ke bore, amma ba a warware matsalolin da sojojin suke gabatar ba. Daga baya, wakilan sojojin sun bukaci yin shawarwari da ministan kula da harkokin tsaron kasa na fadar shugaban kasar Alain Richard Donwahi kai tsaye. (Zainab)