Yang Jiechi ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi nasarar gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa game da shawarar "ziri daya hanya daya" da ya gudana kwanakin baya a nan birnin Beijing, kasashen Larabawa sun ba da muhimmiyar gudummawa, kuma kasar Sin tana son sa kaimi ga samun ci gaba tare da kasashen Larabawa bisa shawarar "ziri daya hanya daya". Sin tana goyon bayan kokarin kasashen Larabawa na tabbatar da 'yancin kabilu, kana tana son ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya. (Zainab)