A kwanakin baya, sarkin Saudiyya da firaministan Isra'ila sun ziyarci kasar Sin. Wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya dai na yayata cewa, Sin ba ta taka muhimmiyar rawa kan batutuwan da suka shafi yankin gabas ta tsakiya, yayin da a yanzu take kokarin shiga harkokin yankin.
Game da wannan batu, Hua Chunying ta bayyana cewa, Sin tana tsayawa tsayin daka kan manufar adalci, tana kuma taka muhimmiyar rawa, wajen warware batutuwan Palesdinu da Isra'ila, da harkar nukiliyar Iran, da batun Syria, da dai sauransu ta hanyar siyasa.
Uwar gida Hua ta ce Sin tana fatan ci gaba da kwazo tare da kasashen dake bin manufar "ziri daya da hanya daya", ciki har da kasashen yankin gabas ta tsakiya, wajen more fasahohi, da zurfafa hadin gwiwarsu, yayin da suke bude kofa da yin mu'amala da juna. (Zainab)