in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta halarci taron shimfida zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya
2017-01-17 19:17:18 cri
An gudanar da taron nemo hanyoyin wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya wanda kasar Faransa ta kira a birnin Paris a ranar 15 ga wata. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana a yau Talata a nan birnin Beijing cewa, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Ming, ya jagoranci tawagar Sin a taro, kana ya gabatar da shawarwari uku, game da matakan sa kaimi ga sake shimfida zaman lafiya a yankin na gabas ta tsakiya.

Hua Chunying ta yi bayanin cewa, shawarwarin da Sin ta gabatar sun hada da sa kaimi ga kasashen duniya da su hada gwiwa wajen tunkarar wasu manyan batutuwan duniya, da kiyaye hanyar tabbatar da shirin shimfida zaman lafiya tsakanin Palesdinu da Isra'ila, da kuma kulawa da batun samun ci gaba a Palesdinu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China