in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kira ga kasashen Iran da Saudiyya da su yi kokarin warware takaddamar da ke tsakaninsu
2016-01-05 19:51:32 cri
Kasar Sin ta bayyana damuwa game da tsamin dangantakar da ke wanzuwa tsakanin kasashen Iran da Saudiya, inda ta yi kira ga kasashen biyu da su yi kokarin warware bambance-bambancen da ke tsakaninsu.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Madam Hua Chunying ta shaidawa taron manema labarai yau a nan birnin Beijing cewa, halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya na cikin rashin tabbas.

Madam Hua ta bayyana fatan kasashen da batun shafa za su yi hakuri tare da kai zuciya nesa. Sannan za su dauki matakan da suka dace, wajen daidaita bambance-bambancen da ke tsakaninsu. Su kuma bunkasa zaman lafiya da kwanciyar hankali ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna ta hanyar la'akari da muradun kasashen da ke shiyyar.

A ranar Lahadi ne kasar Saudiyya ta yanke huldar diflomasiya da kasar Iran, bayan da wasu Iraniyawa masu zanga-zanga suka kona ofishin jakadancin kasar Saudiyya da ke birnin Tehran, domin nuna rashin jin dadinsu da hukuncin kisan da Saudiyya ta yanke kan wani malamin Shi'a Sheikh Nimr Baqir al-Nimr.

A jiya kuma kasashen Bahrai, Sudan da Hadaddiyar daular Larabawa da ke bin mas'habar Sunni suka bi sahun Saudiyya wajen katse huldar jakadanci da Iran, lamarin da ya kara dagula al'amura a shiyyar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China