in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya bukaci da aka ci gaba da tattaunawa don warware rikicin gabas ta tsakiya
2016-02-18 09:43:50 cri
Manzon MDD mai kula da ayyukan wanzar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya Nikolay Mladenov, yayi kira ga kasar Isra'ila da shuwagabannin Falisdinawa, da su hanzarta daukar matakan kawo karshen tashe tashen hankula a yankunan Falasdinawa.

Mr. Mladenov ya ce musayar wuta da dauki ba dadi tsakanin sassan biyu, ba zai haifar da da mai ido ba, don haka kamata ya yi a kai zuciya nesa, tare da komawa teburin shawarwari.

Jami'in wanda ya zanta da manema labaru jiya Laraba a Gaza, yayin ziyarar yini biyu da ya fara a ranar Talata, ya ce manyan burukan al'ummar yankin sun hada da dakatar da kafa shinge da Israila ke yi, da bude mahadar yankunan, tare kuma da aiwatar da kudurin nan na kafa kasashe biyu masu cikakken ikon cin gashin kan su.

A daya bangaren kuma, Mladenov ya bayyana cewa matakin da kungiyar Hamas ta falasdinawa ke dauka na haka hanyoyin karkashin kasa a yankin, da nufin shiryawa yaki da dakarun Isra'ila ba zai magance matsalolin da fararen hula ke fuskanta a yankin ba.

Mladenov, ya jaddada kira ga sassan biyu da su koma teburin shawarwari ba tare da wani bata lokaci ba, kasancewar hakan ne kadai zai bada damar kawo karshen halin kiki-kaka da ake fuskanta tsakanin sassan biyu.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China