Ribar manyan bankunan kasar Sin 5 ta habaka cikin watanni 4 na farkon wannan shekara
Manyan bankuna 5 mallakar gwamnatin kasar Sin, da suka hada da bankin raya masana'antu da ciniki wato ICBC, da bankin bunkasa aikin noma ABC, da bankin kasar Sin, wato Bank of China, da kuma bankin gine gine na kasar Sin CCB da kuma bankin sadarwa na kasar Sin, Bank of Communications a Turance, sun samu karin riba da ta kai kashi 1.68 cikin 100 a watanni hudun farko na wannan shekara.
Wata kididdiga da mahukuntan kasar suka fitar ta nuna cewa, an kiyasta ribar da manyan bankunan 5 suka samu ta tasamma yuan biliyan 267.5 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 38.8 a cikin watanni hudun farko na shekarar ta bana.
Bankin ICBC, shi ne ya samu riba mafi yawa, inda ya ci ribar yuan biliyan 75.786, inda yake kan gaba cikin raguwar bankunan hudu, yayin da shi ma bankin gine gine na kasar Sin wato CCB ya samu karin kashi 3.03 cikin 100. (Ahmad Fagam)