Sun bayyana haka ne jiya Litinin, a wajen taron kasashe dake kewayen Libya karo na 11, wanda ya gudana a Algiers, fadar mulkin kasar Aljeriya.
Wakilan kasashe makwabtan kasar Libya mahalarta taron, sun nuna damuwa kan yadda wasu kasashen waje ke yunkurin daukar matakan soji a Libya, suna masu ganin cewa hakan zai lalata yanayin tsaron da yankin ke ciki.
Don haka suka bukaci a yi musayar ra'ayi tare da gwamnatin kasar Libya, kafin a dauki matakan soja cikin kasar don dakile 'yan ta'adda.
Ban da haka kuma, mahalarta taron sun bukaci bangarorin kasar Libya da su tsagaita bude wuta, tare da rungumar hanyar siyasa da shawarwari wajen daidaita rikicin kasar.
Haka zalika, an jaddada goyon baya ga jama'ar kasar Libya kan kokarinsu na samun masalaha tsakanin al'ummomi daban daban, da burin kafa hukumomi masu karfi a fannonin siyasa, aikin soji, da tsaro, don kare mulkin kasar da cikakken yankinta.(Bello Wang)