Mohamed Gunono, shi ne kakakin rundunar kai dauki gaggawa ta jiragen sama, wadda MDD ke marawa baya, ya ce a halin da ake ciki a yanzu, dambarwar siyasa da kuma samun rarrabuwar kai ya haifar da mayakan na IS suna kara karfi
Gunono yace, bangarorin dake cigaba da takun saka ta fuskar siyasa a kasar basu yin la'akari da yanayin da kasar ta tsinci kanta. Yace bangarorin sun yi sakaci mayakan yan ta'daddan na kokarin yin amfani da rarrabuwar kawunan dake tsakaninsu.
Gwamnatin hadin kan kasar mai samun goyon bayan MDD ta bada sanarwa game da wani yunkuri da take yi na kafa wata rundunar tsaron mayaka 3,000 domin kwace ikon birnin na Sirte.
A ranar 15 ga wannan watan ne gwamnati ta bada sanarwa cewa har yanzu akwai mayakan na IS a yankin na Sirte, duk kuwa da galabar da dakarun gwamnatin suka samu wajen fatattakar yan ta'addan.(Ahmad Fagam)