in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya na yaki da masu fasa kwaurin albarkatun mai
2017-05-01 12:46:15 cri
Mahukunta a kasar Libya sun ce za su dauki dukkanin matakan da suka wajaba, domin yaki da fataucin albarkatun mai a sassan kasar.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin ruwan kasar Ayoub Qassem ya fitar a jiya, ta ce a ranar Juma'ar da ta gabata, dakarun sojin ruwan kasar sun yi nasarar kwace wasu tankokin dakon mai 2, a birnin Zwara bayan musayar wuta da wasu da ake zargin masu fataucin mai ne.

Mr. Qassem, ya ce an kwace tankokin man 2 ne a wani wuri dake da nisan kilomita 2 daga gabar tekun kasar kusa da Zwara a yammacin kasar.

Sanarwar ta kara da cewa, daya daga cikin tankokin man mai dauke da tutar kasar Ukrainia na dauke da tan 3,330 na man dizal. Yayin da na 2 mai tutar kasar Congo, ke dauke da tan 1,236 na man dizal.

Sanarwar ta ce masu fasa kwaurin na cin gajiyar matsalolin tsaro da rikicin siyasa dake addabar Libya, da ke ba su damar fasa kwaurin makamai, da albarkatun mai da ma safarar bil'adama ta barauniyar hanya. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China