in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan Habasha sun ayyana kwanakin zaman makoki domin alhinin wadanda Bola ta hallaka
2017-03-14 20:47:37 cri
Majalisar dokokin kasar Habasha, ta ce za a kwashe kwanaki 3 ana zaman makoki a kasar, domin alhinin rasuwar mutane 72, wadanda zaftarewar laka ta sanya wata tarin shara bunne su, a wata matattarar shara dake wajen birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar.

Duk da cewa an fara fidda tsammanin samun karin wadanda wannan hadari ya shafa da ran su, masu binciken tarin sharar da ta yi ambaliya kan mutane na cewa, mai yiwuwa ne a samu karin mutane binne a wurin da lamarin ya auku, yayin da ake ci gaba da aikin ceto ba dare ba rana.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China