A yayin ganawar tasu, Yang Jiechi ya bayyana cewa, kasar Sin da kasar Habasha su kan nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan dake shafar kasashen biyu, lamarin da ya kare moriyar kasashen biyu yadda ya kamata, har ma da dukkan kasashe masu tasowa gaba daya.
A nasa bangare, Mr. Desalegn ya yabawa kasar Sin kan babban matsayinta cikin harkokin kasa da kasa, ya kuma nuna godiya ga kasar domin taimako da goyon bayan da kasar Sin ta baiwa kasarsa. Haka zalika, ya ce, a matsayin kasa dake kan gaba wadda take yin hadin gwiwa da kasar Sin domin raya harkokin masana'antu da makamashi, kasar Habasha tana maraba da zuwan karin kamfanonin kasar Sin da za su zuba jari a kasar, ta yadda za a cimma moriyar juna.
A wannan rana, Yang Jiechi ya kuma gana da shugaban kasar Habasha Mulatu Teshome, inda suka nuna gamsuwa kan sakamakon da aka samu bisa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasar Habasha, yayin da yin cudanya kan yanayin bunkasuwar kasashen Afirka da kuma dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. (Maryam)