in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta yi gwajin makamai masu linzami
2017-02-05 13:40:02 cri

Kamfanin dillancin labarai na Mehr na kasar Iran ya rawaito cewa dakarun kundunbala na daular Musulunci ta Iran IRGC ta gudanar da shirin gwajin makamai masu linzami karkashin shirinta na tabbatar da tsaron kasa.

Rahotanni sun ce makaman masu linzami sun hada da kirar cikin gida mai tafiyar gajere da matsakaicin zango.

Makaman kirar cikin gida sun hada da samfurin 3-khordad, wanda aka yi gwajinsa a ranar Asabar, yana iya tafiyar nisan kilomita 75, kana zai iya tafiyar kilomita 30 a sararin samaniya.

An gudanar da atisayen sojin na gwajin makamin ne a yanki mai fadin murabbi'in kilomita 35, a yankin Semnan dake arewacin tsakiyar Iran.

Manufar gwajin shi ne domin dakarun na IRGC su samu damar cigaba zama cikin shirin ko-ta-kwana da kuma fuskantar duk wata barazana.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China