An rattaba hannu kan kwangilar ne tsakanin hukumar kula da kafawa da da ayyukan makamashi ta Iran AEOI da kuma Rasha, inda ake dab da fara ginin tashoshin nukiliya guda biyu masu karfin megawatt 1,000.
Wannan jawabin na zuwa ne, bayan shugaban hukumar AEOI Ali Akbar Saleh ya sanar a ranar Asabar cewa, nan bada jimawa ba za a fara ginin tashoshin biyu.
Hamid Chitchian ya kara da cewa, akwai wani aikin dake bisa hanya tsakanin ma'aikatar makamashin da Moscow, inda za a gina tashar makamashi mai karfin nmegawatt 1, 400 a lardin Hormozgan dake kusa da mashigin ruwan Persha, ya na mai cewa tuni aka fara aikin ginin. (Fa'iza Mustapha)