in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ba za ta amince da sake komawa teburin shawarwari game da batun Nukiliyar ta ba
2017-01-18 19:44:52 cri
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, ya ce kasar sa ba za ta amince da sake wata shawara, game da batun Nukiliyar ta ba, duba da cewa tuni aka cimma matsaya game da batun.

Kafofin watsa labarai a Iran din sun rawaito shugaba Rouhani, na ce sake komawa teburin shawara tamkar maida hannu agogo baya ne, kuma yunkuri ne da ba zai haifar da da mai ido ba.

Kalaman na shugaban Iran dai na zuwa ne, bayan da mutumin da ake zaton zai zamo sabon sakataren wajen kasar Amurka Rex Tillerson, ya bayyana aniyar gwamnatin Amurka mai jiran gado, ta sake nazartar batun Nukiliyar kasar ta Iran.

Yayin da yake halartar zaman majalissar dattawan Amurka domin tabbatar da nadin sa, Mr. Tillerson ya tabbatar da amincewar sa, da batun sake duba na tsanaki ga yarjejeniyar da aka cimma da Iran, game da sarrafa sinadarin Uranium.

Kafin nan shi ma shugaban Amurkan mai jiran gado Donald Trump, ya sha furta wasu kalamai dake nuna rashin amincewar sa, da waccan yarjejeniya ta JCPOA da aka cimma da Iran

Yarjejeniyar kasa da kasa ta JCPOA dai, ita ce ta kawo karshen takaddamar da Iran din ta shafe kusan shekaru 10, tana yi da kasashen yamma, don gane da yunkurin ta na sarrafa sinadaran Uranium, shirin da ta sha cewa ba na hada makaman nukiliya ba ne.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China