in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta sanar da kakabawa Iran sabon takunkumi
2017-02-04 10:06:41 cri
A jiya Jumma'a ne ma'aikatar kudin kasar Amurka ta sanar da kakabawa wasu daidaikun mutane sabon takunkumi, don mayar da martini ga gwajin makamai masu linzami da "goyon bayan ta'addanci" da kasar Iran ta yi.

A sanarwar da ta fitar a wannan rana, ma'aikatar ta ce, wadannan daidaikun mutane da kasar ta Amurkar ta sanyawa takunkumi sun gudanar ko sun goyi bayan shirin Iran na harba makamai masu linzami, ko kuma sun tallafawa kungiyar Al-Quds dake karkashin dakarun juyin-juya hali na Iran IRGCn, wadanda za a hana su amfani da dukiya da kadarorinsu dake Amurka, kana za a hana 'yan kasar Amurka su yi cinikayya tare da su.

A nata bangaren, ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayar da sanarwa a wannan rana cewa, tana adawa da matakin Amurka na sanya takunkumi kan wasu daidaikun mutane bisa dalilin gwajin makamai masu linzami. Sanarwar ta ce, kasar Iran ta yi nazari kan makamai masu linzami ne da nufin kiyaye tsaron kasar ta, wadanda ke daukar makamai na yau da kullum kawai. Kuma tana da 'yanci kamar yadda tsarin dokokin MDD suka tanada. Duk wani tsoma baki da wasu kasashe suka yi tamkar keta dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar makaman nukiliyar Iran ne. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China