Za'a kara raya layin dogon da ya hada Tanzaniya da Zambiya, in ji ministan harkokin wajen Sin
Jiya Lahadi, yayin da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na kasar Zambiya Harry Kalaba ke ganawa da manema labarai a birnin Lusaka, Wang ya ce, layin dogon da aka shimfida tsakanin kasashen Tanzaniya da Zambiya shekaru da dama da suka gabata, hanya ce dake shaida dadadden zumunci da 'yanci a nahiyar Afirka.
Sin na fatan nuna kwazo tare da Zambiya da Tanzaniya, domin kara inganta wannan layin dogo har ya zama hanyar hadin-gwiwa dake bunkasa sosai.(Murtala Zhang)