in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya yi shawarwari da takwaransa na Zambiya
2017-01-09 10:11:46 cri

A jiya Lahadi 8 ga watan nan ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Zambiya Harry Kalaba. Yayin ganawar tasu, Mr. Wang ya ce, Sin na fatan taimakawa Zambiya wajen neman ci gaba bisa karfinta, har ta zama mahadar sufuri, kuma cibiyar zirga-zirgar kaya dake nahiyar Afirka.

A nasa bangaren kuma, Mista Kalaba cewa ya yi, kasarsa na fatan karfafa hadin-gwiwa tare da kasar Sin a fannin yin kwaskwarima, da farfado da layin dogon da aka gina tsakanin Tanzaniya da Zambiyar, matakin da zai kara taka muhimmiyar rawa wajen raya masana'antun kasar Zambiya, gami da dinkewar tattalin arzikinsu bai daya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China