A makon da ya gabata ne hadakar kungiyoyin al'umma a kasar suka kaddamar da wani gangami domin matsawa gwamnati shirya kada kuri'a kuri'ar raba gardama kan kafa dokar kare hakkokin al'umma, bayan wanda aka yi tare da babban zaben kasar a shekarar da ta gabata ya lalace.
Kungiyoyin da daidaikun mutane na fafutukar tabbatar da bin ka'idojin doka da kuma sanya kudurin dokar fadada hakkokin al'umma cikin kundin tsarin mulkin kasar da aka yi wa gyaran fuska. ( Fa'iza Mustapha)