Tuni dai shugabar rundunar Kakoma Kanganja, ta fidda takardar umarnin, tana mai cewa sashe na 3 da na 5 na doka ta 103, ta ayyukan 'yan sanda ta tanaji wannan mataki, sai dai kuma da yawa daga jami'an rundunar na yin watsi da dokar.
Uwar gida Kanganja, ta ce mai yiwuwa masu leken asiri na kasashen waje, su yiwa kasar kutse ta hanyar auren jami'an 'yan sanda, wanda hakan zai iya bada damar bankadar sirikan kasar cikin sauki.
Tuni dai wannan umarni ya fara shan suka daga wasu 'yan kasar, wadanda suke ganin aiwatar da shi ba shi da wata fa'ida.(Saminu Alhassan)