in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Mauritius
2017-05-18 10:48:30 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Mauritius Seetanah Lutchmeenaraidoo jiya Laraba 17 ga wata, wanda ya zo Beijing don ziyarar aiki da kuma halartar taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar "Ziri daya hanya daya".

Yayin ganawar Mr. Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin na farin cikin ganin yadda Mauritius ke raya kanta har ma ta zama wata gada a tsakanin Sin da Afirka yayin da ake kokarin samun ci gaba bisa shawarar "Ziri daya hanya daya".

A nasa bangaren, Mr. Lutchmeenaraidoo ya bayyana cewa, kasarsa na da aniyar ci gaba da samun fahimta da amincewar juna a tsakanin bangarorin biyu a kan batutuwan da ke da nasaba da babbar moriyarsu da wadanda ke jawo hankalinsu. Kana ana son inganta hadin gwiwar kasashen biyu bisa shawarar "Ziri daya hanya daya".(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China