Liu Yandong ta bayyana haka ne a ranar Talata, yayin tattaunawar da ta yi a mabanbantan lokuta da Babban Darktan UNICEF Anthony Lake da takwaransa na hukumar UNFPA Babatunde Osotimehin, wadanda suka halarci taron shawarar 'ziri daya da hanya daya' dake da nufin karfafa hadin gwiwa da kasashen duniya, wanda ya gudana a ranakun 14 da 15 na watan Mayu, a nan birnin Beijing.
Shawarar ziri daya da hanya daya na da nufin samar da kyakkyawan yanayin samun ci gaban tattalin arzikin yankuna da duniya baki daya, da taimakawa kasashen da ke kan hanyar da shawarar ta shafa amfana daga dammamakin da ci gaban kasar Sin ta samar tare da samun ci gaba na bai daya.
Da suke jinjinawa irin nasarori da kasar Sin ta samu wajen kare hakkokin yara da ciyar da al'umma gaba, da kuma taya ta murnar nasarar da taron ziri daya da hanya daya ya samu, Anthony Lake da Bababtunde Osotimehin, sun ce a shirye suke su karfafa hadin gwiwa da kasar Sin karkashin shawarar, ta yadda za a samu damar cimma muradun ci gaba masu dorewa kawo shekarar 2030. (Fa'iza Mustapha)