Bayanin ya bayyana cewa, shugaba Kenyatta ya bayyana a gun taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa na "ziri daya hanya daya" da aka gudanar, a cibiyar taruruka ta kasa da kasa dake nan birnin Beijing cewa, yayin da ake aiwatar da shawarar hada kan duniya da Sin ke taka muhimmiyar rawa wajen aiwatarwa, kasashen Afirka suna da damar sake rike damar da suka rasa a da a duniya.
Ya ce shawarar "ziri daya hanya daya" da Sin ta gabatar, ta dace da ajandar shekarar 2063 da kungiyar AU ta gabatar, wato hada kan ayyukan more rayuwa a nahiyar Afirka.
Bisa bayanin, shugaba Kenyatta ya bayyana cewa, "ziri daya hanya daya" ta samar da damar canja tsarin tunani a nahiyar Afirka, kuma tilas ne kasashen Afirka sun canza daga masu shigar da kayayyaki zuwa masu fitar da su. (Zainab)