in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jiragen sama daga Sin sun fara isa kasashe 43 da suka amince da shawarar ziri daya hanya daya
2017-05-17 09:41:00 cri

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasar Sin, ta ce yanzu jirage daga kasar Sin sun fara tashi kai tsaye zuwa kasashe 43 da suka amince da shawarar ziri daya hanya daya.

A cewar jami'in hukumar Wang Changyi da ya bayyana haka a jiya Talata, kimanin tashin jirage 4,200 ake samu a kowane mako zuwa kasashen.

A karshen shekarar 2016 ne kasar Sin ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyin sufurin jiragen sama da gwamnatocin kasashe da yankuna 120, inda kasashen da suka amince da shawarar ziri daya hanya daya, suka mamaye fiye da rabin adadin.

A watanni 4 na farkon shekarar nan, jigilar fasinjoji daga kasar Sin zuwa wadannan kasashe, ya tashi daga kashi 39.8 a shekarar 2015, zuwa kashi 47.1 cikin dari.

An samu kyautatuwar al'amuran ne saboda nasarorin da aka samu bisa shawarar da kasar Sin ta gabatar a shekarar 2013 game da ziri daya hanya daya, wadda ke da nufin hada nahiyar Asiya da Turai ya dangana zuwa Afrika na nufin bunkasa daddadiyar hanyar cinikayya da ta ratsa yankunan.

An kammala taron yini biyu na shugabannin duniya a ranar Litinin, inda aka dauki alkawura da kyawawan fata da dama, ciki har da rattaba hannun kan jerin yarjejeniyoyin da ke da nufin farfado da hanyar siliki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China