Rahotanni na nuna cewa, a kwanakin baya, kasashen duniya na yaba wa wannan taron kolin dandalin tattaunawar shawarar Ziri daya da hanya daya, amma akwai wasu kafofin yada labaru kadan dake cewa, kasar Sin ta shirya wannan taro ne domin yunkurin daga matsayinta ko karfinta na shugabanci a kasashen duniya kawai. Game da irin wadannan maganganu, madam Hua Chunying ta ce, kasar Sin ce ta ba da shawarar Ziri daya da hanya daya, amma a kullum tana martaba ka'idar "tattaunawa, da samun ci gaba tare, da kuma samun moriya tare". A ganin kasar Sin, dukkan kasashen duniya manya ko kanana dukkansu daidai suke. Sannan tana ganin cewa, babbar kasar dake da karin albarkatu da karin karfi, ya kamata ta sauke karin alhakin da aka dora mata, kuma ta bayar da karin gudummawa. Kasar Sin ta gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya, har ma ta shirya taron kolin dandalin tattaunawa kan shawarar domin sauke irin wannan nauyin da aka dora mata kawai. (Sanusi Chen)