A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, Kenya na daga cikin kasashen Afirka da ake gwajin hadin gwiwar masana'antu a tsakaninsu da Sin, wadda kuma ke zama abin koyi a hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka. Ya ce, kasarsa tana fatan hada kai da kasar Kenya domin daga matsayin dantankatar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.
Uhuru Kenyatta daga nasa bangaren ya ce, taron dandalin da aka gudanar a wannan karo ya nuna wa duniya baki daya nasarorin da aka samu a shawarar ziri daya hanya daya, wanda kuma ya samar da dandalin da kasashe masu tasowa da kuma masu sukuni za su rika tattauna yin hadin gwiwa bisa tushen samun moriyar juna. Kenya tana son shiga a dama da ita wajen raya "ziri daya hanya daya", tare da karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin tattalin arziki da zuba jari da makamashi da yawon shakatawa da kuma muhimman ababen more rayuwa. (Lubabatu)