in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Buhari ya tafi waje don ganin likita
2017-05-08 10:20:16 cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi birnin London a daren ranar Lahadi don ganin likitansa.

An bayyana haka ne cikin wata sanarwar da kakakin shugaban kasar Femi Adesina ya sanyawa hannu. Jami'in ya bayyana cewa, da farko shugaba Buhari ya yi shirin tashi zuwa London da yammacin ranar Lahadi, amma daga bisani ya jinkirta domin karbar 'yan matan Chibok 82 da aka sako su, wadanda suka isa Abuja da yammacin ranar a Lahadin.

Sanarwar ta ambato shugaba Buhari, yana wa jama'ar Najeriya cewa babu bukatar su nuna damuwa.

A cewar Adesina, likitoci ne kadai za su iya tabbatar da tsawon lokaci da shugaban zai shafe a birnin London, sai dai a lokaci guda mataimakin shugaban kasar ne zai ci gaba da jan ragamar harkokin mulki a kasar.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China