Kwamitin sulhun MDD yayi Allah wadai da kai hari kan jami'an wanzar da zaman lafiya a CAR
2017-05-16 14:18:30
cri
A yau Talata kwamatin sulhun MDD yayi Allah wadai da babbar murya game da mummunan harin da aka kaddamar kan tawagar jami'ai na MDDr, da fararen hula, da kuma ma'aikatan jin kai a jamhuriyar tsakiyar Afrika CAR, harin da ya rutsa da wani jami'in wanzar da zaman lafiya dan kasar Morocco.(Ahmad Fagam)