Zaben wanda ya gudana cikin lumana da samun fitowar 'yan kasar soai suka kada kuri'ansu, in ji Frahan Haqq, mataimakin kakakin majalissar a ganawarsa da manema labarai, yana mai misali da sanarwar hadin gwiwwa ga manema labarai da majalissar ta yi tare da kungiyar AU, da kungiyar tarayyar tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afrika ECCAS, kungiyar tarayyar kasashen Tuari EU da kungiyar kasashen renon Faransa La Francophonie a ranar Jumm'a.
Hukumomin gaba dayan su sun mika sakon taya murnan su ga zababben shugaban kasar Faustin-Archange Touadera, inda suka bayyana goyon bayan su bisa ga kudurin shi na inganta tattaunawa da sulhu a cikin kasar, in ji Farhan Haq.
Hukumomin kasashen duniyan za su ci gaba da ba da goyon bayansu ga sabon kokarin da kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ke yi yadda ya kamata, in ji shi. (Fatimah Jibril)