Shugaba Xi Jinping na kasar Sin wanda ya jagoranci zagayen tattaunawar, ya bayyana cewa, shugabannin sun amince cewa, za su karfafa hadin gwiwar kasa da kasa game da yadda za a bunkasa shawarar ziri daya hanya daya, sannan za su hada gwiwa wajen tunkarar kalubalen dake fuskantar tattalin arzikin duniya.
Ya kuma bayyana a yayin da yake jawabin rufe taron kolin cewa, shugabannin sun goyi bayan tsarin raya tattalin arziki na gajeren lokaci da yadda za a bunkasa manyan tsare-tsare a kokarin cimma bunkasuwa tsakanin kasashen duniya.
Bugu da kari, sun bayyana fatan gina wata gada da za ta samar da kafar musaya tsakanin jama'a da kuma yadda za a inganta rayuwar jama'a baki daya. (Ibrahim)