Ya ce, wadannan sakamakon da dandalin ya cimma, za su kara taimakawa wajen gina ziri daya da hanya daya, sannan zai karfafa gwiwar dukkan bangarorin da shawarar ta shafa kan yadda za a inganta hadin gwiwa.
Shugaba Xi ya shaidawa manema labarai a karshen dandalin farko na shawarar a nan birnin Beijing cewa, kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 68 ne suka sanya hannu kan yarjeniyoyin hadin gwiwa da kasar Sin game da Ziri daya hanya daya. Kana an cimma sakamako sama da 270 a yayin taron.(Ibrahim)