Jami'ar kasar Mozambique: a daidaita shirye-shiryen raya tattalin arziki don biyan bukatun jama'ar kasa da kasa
Nyeleti Mondiane, ita ce mataimakiyar ministar harkokin wajen kasar Mozambique, wadda take halartar taron dandalin koli na hadin gwiwar kasa da kasa ta fuskar shawarar "ziri daya hanya daya" a birnin Beijing na kasar Sin. Yayin da take hira da wakilin CRI a jiya Lahadi, ta ce shugaban kasar Sin Xi Jinping, a cikin jawabinsa, ya nuna aniyar da kasar Sin ta dauka, wajen kokarin aiwatar da shawarar "ziri daya hanya daya", tare da ambatar kalubalolin da duniyarmu ke fuskantar. A cewar jami'ar kasar ta Mozambique, kamata ya yi, a yi kokarin daidaita shirye-shiryen raya tattalin arziki na kasashe daban daban, ta yadda jama'ar kasa da kasa da su samu alfanu.(Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku