Yayin wata ganawa da shugaban bankin duniya a jiya Lahadi, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce yanzu haka ana ci gaba da gudanar da sauye sauye ga tattalin arzikin Sin, matakin da ke bukatar sauya akalar masana'antu bisa tsarin gargajiyar kasar, matakin da zai habaka ci gaba cikin sauri.
Har wa yau Li Keqiang, ya shaidawa Jim Yong Kim cewa, kasar sa na fatan karfafa hadin gwiwa da babban bankin duniya, wajen gudanar da bincike game da hanyoyin samar da bunkasuwa, da na sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin kasashen duniya.
Ya ce, a matsayin ta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, Sin na da burin sauke nauyi dake kan ta, na daukar matakai mafiya dacewa a fannin rage talauci, da hada karfi da karfe da masu ruwa da tsaki, da nufin samar da ci gaba.
A hannu guda kuma, ya yi imanin cewa, babban bankin duniya na da ikon jagorantar kasashen duniya, wajen aiwatar da manufofin da za su dunkule tattalin arzikin duniya, da cimma moriya ta bai daya.
A nasa bangare, Mr. Kim cewa ya yi, babban bankin duniya na da yakinin cewa, Sin na aiki tukuru wajen aiwatar da sauye sauye, da bunkasa kirkire kirkire, da samar da dama ta habaka ci gaba. Kaza lika bankin na duniya zai ci gaba da hadin gwiwa da Sin a wadannan fannoni.(Saminu)