A cikin jawabinsa, shugaban ya nanata bukatar tsayawa kan kiyaye zaman lafiya da yin hadin gwiwa, da bude kofa, da nuna hakuri, da koyon fasahohi na juna, da kokarin tabbatar da moriyar juna.
Bayan sauraron wannan jawabi, gamayyar kasa da kasa sun jinjinawa kalaman na shugaba Xi, gami da nuna amincewa kan manufar kasar Sin, tare da fatan hadin kai tare da kasar, don raya duniyarmu.
A cewar wani masani mai suna Melaku daga cibiyar nazarin manyan tsare-tsare a fannin huldar diplomasiyya ta kasar Habasha, kasar Sin ta taimakawa Habasha, da sauran kasashen dake Afirka a fannin gina kayayyakin more rayuwa, gami da zuba makudan kudi ga kasashen, lamarin da ya kyautata yanayin zirga-zirga, da muhallin zuba jari a Afirka, ta yadda ya zama tallafi ga kasashen Afirkan kan kokarinsu na raya masana'antu.
Sa'an nan, cikin dukkan ayyukan da kasar Sin ta gudanar a nahiyar Afirka, ba ta taba tilastawa wani ya bi ra'ayin ta ba, ko kuma hanyar da take bi wajen raya kasa. Sabanin haka, ta kan karfafa wa kasashen Afirka gwiwarsu, wajen zabar hanyar da za su bi domin raya kasa da kansu, bisa yanayin da kasashen suke ciki.(Bello Wang)