Yayin ganawarsu, Wang Yi ya ce, jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar wajen bikin budewar taron, ya shaida aniyar kasar Sin ta raya "ziri daya hanya daya" bisa manufar zaman lafiya, da neman samun walwala, da bude kofa, da kokarin kirkiro sabbin fasahohi. Hakan, a cewar ministan kasar Sin, ya tabbatar da hanyar da za a bi, wajen zurfafa hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.
Ministan ya kara da cewa, Kenya wata muhimmiyar kasa ce a nahiyar Afirka, wadda kasar Sin ta fara da hadin gwiwa tare da ita a fannin raya masana'antu, don haka yana da imanin cewa, kasar Kenya za ta zama kan gaba tsakanin kasashen Afirka, a kokarin aiwatar da shawarar "ziri daya hanya daya".(Bello Wang)