Daga cikinsu kuma, firaministan kasar Habasha Hailemariam Dessalegn, ya yaba da gwamnatin kasar Sin, musamman ma shugaba Xi Jinping na kasar, game da basirar da ya nuna, a jawabinsa na bude dandalin tattaunawar, inda ya ambato fannin karfafa hadin gwiwar kasa da kasa, da inganta wadatuwar duniya baki daya. Yana mai cewa, shawarar "Ziri daya hanya daya", na dacewa sosai da muradun samun dauwamammen ci gaba na MDD kafin shekarar 2030, da kuma ajandar nan da shekarar 2063 ta nahiyar Afirka, wadda za ta samar da gajiya ga duk duniya baki daya.
A gun cikakken taron, wakilai mahalartan taron da suka fito daga kasashen Burtaniya, da Faransa da kuma Jamus, sun bayyana amincewa da goyon baya ga shawarar "Ziri daya hanya daya. (Bilkisu)