Shugaban Turkiyya: "ziri daya hanya daya" zai zama hanyar wanzar da zaman lafiya da samun nasarar juna
A gun bikin bude babban taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa kan "ziri daya hanya" da aka gudanar a yau Lahadi a nan birnin Beijing, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya gabatar da jawabi, inda ya ce, shawarar "ziri daya hanya daya" za ta taka muhimmiya rawa, ta fannin kyautata manyan ababen more rayuwa, da fasahohi na kasashen da shawarar ta shafa, tare da fadada hanyoyin kasa da na ruwa, da kuma na sama, wadanda da suka hada nahiyoyi daban daban.(Lubabatu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku