A jawabin da ya gabatar, Mr. Putin ya ce shiyyar Asiya da Turai na dunkulewa yadda ya kamata, kuma ana kokarin aiwatar da shirye-shirye da dama.
Ya ce, kasashe mambobin kungiyar tarayyar tattalin arzikin Turai da Asiya, na goyon bayan shawarar "ziri daya hanya daya". Kuma shawarar da shugaban kasar Xi Jinping ya gabatar a jawabinsa na bude taron dangane da hadin gwiwar kasa da kasa ta fannonin makamashi da zirga-zirga, da manyan ababen more rayuwa, da masana'antu, da kuma al'adu, ta kasance tamkar faduwa wadda ta zo daidai da zama. Wanda kuma hakan ke dada karfafa matsayin kasar Sin game da batun dunkulewar shiyyar. (Lubabatu)