in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya gana da shugaba Putin
2017-05-14 15:55:59 cri

Yau 14 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, wanda ke halartar babban taron tattaunawar hadin gwiwa ta kasa da kasa game da shawarar "ziri daya hanya daya" a nan birnin Beijing, inda Xi ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashen biyu wato Sin da Rasha su sanya kokari tare domin raya huldar dake tsakanin sassan biyu.

Tun daga watan Mayun shekarar 2015, Sin da Rasha suka cimma matsaya guda kan manufar shawarar "ziri daya hanya daya" da aikin kawancen tattalin arzikin kasashen Asiya da Turai waje daya, kuma suna gudanar da aikin lami lafiya a cikin shekaru biyun da suka gabata, har ma sun samu sakamako a bayyane, a nan gaba kuma, kasar Sin tana son ci gaba da yin kokari tare da Rasha domin ciyar da aikin gaba yadda ya kamata.

A nasa bangaren, tun da farko shugaba Putin, ya taya murnar bude wannan taron kolin tattaunawar hadin gwiwar tsakanin kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya hanya daya" cikin nasara, kana ya jinjnawa kokarin da kasar Sin take yi a fannin gabatar da shawarar tare kuma da shirya wannan dandalin, saboda a cewarsa hakan zai sa kaimi game da yin cudanya da hadin gwiwar tattalin arziki dake tsakanin kasa da kasa. Putin ya kara da cewa, ya yi farin ciki matuka da ganin ana gudanar da huldar dake tsakanin Sin da Rasha kamar yadda ya dace.

Kazalika, shugabannin kasashen nan biyu sun yi musanyar ra'ayoyi tsakaninsu kan manyan batutuwan kasa da kasa da kuma na shiyya shiyya wadan da suka fi jawo hankulansu duka, kamar yanayin da zirin Korea ke ciki a halin yanzu da dai sauran muhimman batutuwa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China