Sakatare-janar na MDD: Inganta alaka tsakanin shawarar "ziri daya hanya daya" da shirin neman ci gaba mai dorewa nan da shekara ta 2030 na da muhimmanci
A wajen babban taron dandalin tattaunawar hadin-gwiwar kasa da kasa kan "ziri daya hanya daya", wanda aka bude yau Lahadi a nan birnin Beijing, sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, Mista Antonio Guterres ya bayyana cewa, duk da cewa akwai bambanci tsakanin shawarar "ziri daya hanya daya" da shirin neman ci gaba mai dorewa nan da shekara ta 2030, a hannu guda burinsu iri daya ne, wato neman ci gaba mai dorewa, da kokarin samar da zarafi na samun moriya tare.
Haka kuma, dukkansu na maida hankali kan karfafa mu'amala da cudanya tsakanin kasa da kasa, da kuma yankuna daban-daban, ciki har da daidaita manufofi, hade ababen more rayuwa, kasuwanci maras kaidi, hade sassan hada hadar kasuwanci da kulla alaka tsakanin al'ummu.
Antonio Guterres ya jaddada cewa ko shakka ba bu, karfafa alaka tsakanin shawarar "ziri daya hanya daya" da shirin MDD na neman ci gaba mai dorewa nan shekara ta 2030, na da matukar muhimmanci. (Murtala Zhang)