in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da UNESCO sun amince su hada gwiwa a fannin raya shawarar "ziri daya hanya daya"
2017-05-14 11:25:19 cri

Kasar Sin da hukumar raya ilimi da kimiyya da al'adu ta MDD UNESCO, sun amince da hada gwiwa, wajen tabbatar da nasarar shawarar ziri daya da hanya daya.

Da yake tabbatar da hakan yayin zantawar sa da babbar daraktar UNESCO, Irina Bokova, mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong, ta ce batun musaya tsakanin al'ummu, na daya daga muhimman sassa cikin shawarar ziri daya hanya daya, wadda kuma jigo ne na manyan manufofin UNESCO.

Bokova dai ta iso nan birnin Beijing, domin halartar taron dandalin tattaunawa na hadin gwiwar kasa da kasa kan "ziri daya hanya daya" da tuni aka bude a Lahadin nan.

Da take bayyana jin dadin ta game da irin dadadden goyon baya da Sin ke baiwa UNESCO, jami'ar ta ce, da yawa daga manufofin da kasar Sin ke gabatarwa sun zamo abun misali ga duniya, kuma UNESCO na fatan hada gwiwa da Sin, karkashin wannan manufa ta ziri daya hanya daya, domin tabbatar da nasarar muradun ci gaba mai dorewa nan da shekara ta 2030.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China