Babban darakta a ofishin shirin samar da abinci da aikin gona na MDD Jose Graziano da Silva, ya bayyana shawarar "ziri daya hanya daya", a matsayin wata kafa da za ta samar da zarafi na samar da ci gaba, don haka ya dace a hade shawarar da kudurorin ci gaba masu dorewa na MDD, wadanda ake fatan cimmawa nan da shekarar 2030.
Mr. Graziano da Silva, ya bayyana hakan ne ga wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, manufar ziri daya hanya daya, ta zarce batun cinikayya da zuba jari kadai, duba da cewa manufar tana karfafa hadin gwiwa, tare da kare al'adu, da samar da ci gaba mai dorewa.
Mr. Graziano wanda aka gayyata domin ya halarci taron dandalin koli, na hadin gwiwar kasa da kasa karkashin shawarar "ziri daya hanya daya", wanda zai gudana a ranekun 14 da 15 ga wannan wata, ya jinjinawa manufar, yana mai cewa, kasashe da dama da kungiyoyin kasa da kasa, na ci gaba da rungumar wannan shawarar.
Jami'in na FAO ya ce, yayin taron na yini biyu, zai maida hankali ga batun bunkasa ci gaban kasashen masu tasowa, da matakan bunkasa yankunan karkara, da kuma harkar raya noma, da dakile matsalar karancin abinci da kare gurbatar sa.(Saminu)