in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude babban taron dandalin tattaunawar kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya hanya daya"
2017-05-14 11:21:19 cri

Yau Lahadi an bude babban taron dandalin tattaunawar kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya hanya daya" a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude taron kuma ya bayar da wani muhimmin jawabi, inda ya kirayi bangarori daban daban su sanya kokari tare domin tabbatar da shawarar, ta yadda za a cimma burin samun wadata da bude kofa da kirkire-kirkire da kuma wayewar kai. Mista Xi ya jaddada cewa, kasar Sin tana son kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da daukacin kasashen da suka shiga shawarar "ziri daya hanya daya" bisa tushen ka'idoji biyar na yin zaman tare cikin lumana, ba zai yiyu ba kasar Sin ta tsoma baki a cikin harkokin gida na sauran kasashe, kuma ba zai yiyu ba kasar Sin ta tilasta wa sauran kasashen duniya su yi amfani da tsarin zaman takewar al'ummarta da tsarin bunkasuwarta, tana sa ran za ta samu ci gaba tare da sauran kasashen duniya baki daya.

Shugaba Xi ya ci gaba da cewa, tun bayan da kasar Sin ta gabatar da shawarar "ziri daya hanya daya" a shekarar 2013, kawo yanzu wato a cikin shekaru hudu da suka gabata, kasar Sin da kasashen da abin ya shafa suna kara zurfafa cudanyar dake tsakaninsu a fannoni daban daban, misali, manufofin raya kasa, da gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, da cinikayya, da musanyar kudade, da kula al'adu. Tsakanin shekarar 2014 da ta 2016 kuwa, kwatankwacin adadin kudin da aka samu daga wajen cinikiyyar dake tsakanin kasar Sin da kasashen dake da nasaba da shawarar "ziri daya hanya daya" ya kai dalar Amurka biliyan dubu 3, kana adadin jarin da aka zuba ya zarta dala biliyan 50. Kaza lika, kamfanonin kasar Sin sun samar da kudin shiga daga harajin da aka biya kusan dala biliyan 1 da miliyan 100, da guraben aikin yi dubu 180 a kasashen. Hakan ya nuna cewa, shawarar "ziri daya hanya daya" ta biya bukatun ci gaban kasashen duniya, kuma ta dace da babbar moriyar al'ummomin kasashen duniya, ko shakka babu akwai tana da makoma mai haske.

Shugaba Xi ya sanar da matakan da kasar Sin za ta dauka domin sa kaimi kan gudanarwar shawarar "ziri daya hanya daya". Misali, kasar Sin za ta kara zuba jarin da yawansa zai kai RMB yuan biliyan 100 ga asusun hanyar silikin da aka kafa musamman ma domin shawarar, kuma kasar Sin za ta sa kaimi ga hukumomin kudin kasar, domin su gudanar da ayyukansu a kasashen ketare. An yi hasashen cewa, ayyukan za su shafi kudin Sin RMB kusan biliyan 300. Ban da haka kuma, bankin raya kasa na kasar Sin zai samar da rancen kudin yuan biliyan 250, haka kuma bankin shige da fice na kasar Sin, zai samar da rancen kudin yuan biliyan 130, domin nuna goyon bayansu kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen dake karkashin shawarar "ziri daya hanya daya".

Ban da haka kuma, kasar Sin za ta samar da taimakon kudin da yawansa zai kai yuan biliyan 60 ga kasashe masu tasowa, da kungiyoyin kasa da kasa da suke da nasaba da shawarar "ziri daya hanya daya", domin kara kyautata zaman rayuwar al'ummar kasashen.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China