Da safiyar yau Lahadi 14 ga watan Mayun nan ne aka bude babban taron dandalin tattaunawa na hadin gwiwar kasa da kasa kan "ziri daya hanya daya", inda shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping ya halarci taron, ya kuma gabatar da muhimmin jawabi.
Babban taken taron da aka bude a nan birnin Beijing na kasar Sin shi ne, inganta hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, da neman ci gaba mai kawowa juna moriya.
Shugabanni gami da kusoshin gwamnatocin kasashe 29, tare kuma da shugabanni gami da wakilai na Majalissar Dinkin Duniya, da na Bankin Duniya, da wakilan asusun ba da lamuni na duniya su sama da 70, da kuma kwararru daga bangarorin siyasa da cinikayya sun halarci bikin.
Wannan taron da aka bude a yau, ya kasance babban taro na kasa da kasa mafi kasaita da kasar Sin ta shirya, tun bayan da shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawara ta "ziri daya hanya daya" a shekara ta 2013.
A yayin taron dandalin tattaunawar, mahalartan sa za su gudanar da shawarwari, da tattaunawa dangane da muhimman kalmomi biyu, da suka hada da "hadin gwiwa" da "cin moriya tare", da sauran wasu muhimman batutuwa, ciki har da inganta mu'amala ta fuskar manufofi, da yin cinikayya ba tare da matsala ba, da yin musanyar kudade, da mu'amalar jama'a da makamantansu.(Murtala Zhang)